Part _02
Azahiri nakanji tsoro acikin Raina abinka da sabon shiga soyayya Kuma mai tsoran mata nakan tambayi Kaina meyasa zuciyata ke kokarin sani a wahala saboda a tunanina soyayya wahalace yaudai antashi daga makaranta Dan haka nabarwa gobe Amma duk da haka zuciya ta Bata daina tunanin kyakkyawar fuskar datayi tubali da ita tabbas so makahone Domin kuwa naga tsayin Daren ranar jinshi nake tamkar gari bazai wayeba haka na shafe tsawon Daren banyi barciba gari na wayewa bayan nayi Sallah nafara Shirin makaranta bayan nayi wanka nagama shiryawa naje nagaida mamana da babana tare da Yi musu sallama zantafi makaranta abinka da iyaye jigon rayuwa Suka ce dani Allah ya tsare Suka samin albarka na fito cikin farin ciki na nufi baking titi Dan Hawa mota zuwa makaranta yaukan nazo dawuri fiyeda kullum
Na shiga aji mutum bakwaine 7 ne aciki harni na takwas na dauki Wani Dan karamin littafi na turanci ina karantawa tsawon mintuna Sha biyar naji sallama na amsa tare da dago Kai abokina Abba ne yace yaufa kazo da wuri nayi murmushi tare da tambayar sa ina sadiya take naga yau Bata zoba yace eh may be tana hanya ne nace toh Allah yakawota Lafiya yace Ameen nafara tunanin fadamasa Amma sam nakasa fada idan nayi kokarin fadamasa sai Wata zuciyar tace a'a kabari bayanzuba Wata Kuma tace kafada masa.....
Yanzu dai Muna jiran isowar sadiya
Muhadu a part 03